Me ka ke nema?


Shafin Farko

Majalisar Wakilai - Amurka



Majalisar Wakilan Amurka   Hoto:U.S. House of Reps


Gabatarwa

Majalisar Wakilai, ɗaya ce daga cikin tagwayen majalisun Tarayyar Amurka wadda Kundin Tsarin Mulkin Amurka ya ɗorawa wasu nauye-nauye na musamman waɗanda suka bambanta da na Majalisar Dattawa. Majalisa ce da aka kafa ta da nufin ta kasance ta jama’a, saboda haka, kai tsaye jama’a suke zaɓo mambobinta daga jahohi.

Wannan Majalisa ta Wakilai ita take ƙirƙirar dokokin gwamnatin tarayya tare kuma da bata hanya ta wuce domin a aiwatar da ita.

Mambobin Majalisa

Sashe na biyu (Section 2) na kashin farko na Kundin Tsarin Mulkin Amurka ya ce: "Majalisar Wakilai (House of Representatives) ta ƙunshi mambobin da jama'a suka zaɓa a duk cikin shekara ta biyu daga jama'ar mabambantan jahohi, kuma wanda aka zaɓa daga kowace jaha ya zama ya cika dukkan sharuɗɗan mabambantan majalisun jahohi"

Majailsar tana da mambobin da yawansu yakai 435 da ake zaɓo su daga jahohi tare da la’akari da yawan jama’ar jahar. Abin nufi, yawan wakilan da za su wakilci jaha a wannan zauren majalisa ya dogara da yawan jama’ar da jahar take da su.

Sai dai, akwai mutane biyar da ke wakiltar mazaɓar Colombia, Virgin Island, Guam, American Samoa, da kuma Commonwealth of the Northern Marian Island. Sai kuma kwamashinan cikin gida (resident commissioner) da ke wakiltar Puerto Rico.

Wakilai

Wakilai, wato Representatives, waɗanda kuma ake kira da congressman ko congresswoman, su ne mutanen da ake zaɓowa domin wakiltar wata mazaɓa daga cikin mazaɓun ‘yan Majalisar Wakilai da adadinsu ya kai 435.

Sharuɗa

Shuraɗan tsayawa takarar neman sahalewar jama’a domin yin wakilci a wannan majalisa ta wakilan Amurka guda uku ne kacal, kamar yadda Kundin Tsarin Mulkin Amurka ya tanada. Kundin ya ce: "Babu wani mutum da zai zama wakili wanda bai kai shekaru 25 da haihuwa ba, kuma ya zama ɗan ƙasar Amurka na tsawon shekaru bakwai, wanda kuma bai zama mazaunin jahar da zai wakilta ba idan aka zaɓe shi". Abin nufi, a cika waɗannan sharuɗa uku kamar haka:

  1. Zamowa ɗan shekara 25.
  2. Zamowa ɗan ƙasar Amurka na tsawon shekaru 7.
  3. Mazaunin jahar da za a wakilta.

Wannan fa shi ne a ci bilis. Kenan a yau idan ka dira a Amurka ka samu takardar sahelwar zama ɗan ƙasa, to bayan shekaru bakwai idan shekarunka basu gaza 25 ba za ka iya tsayawa takara. Matuƙar dai jama'ar jahar sun zaɓe ka, to kai fa ruwa ta sha.

Manazarta

Library of Congress (Babu Shekara). About the Congress. An ciro a 2021, daga https://www.congress.gov/about

The White House (Babu Shekara). The Legislative Branch. An ciro a 2021, daga https://obamawhitehouse.archives.gov/1600/legislative-branch

United State House of Representatives (Babu Shekara). The House Explained. An ciro a 2021, daga https://www.house.gov/the-house-explained


Koma Babban Shafin Tarihi
Babban Shafin Nijeriya


Tura wannan shafi zuwa ga abokai ta:


Latsa madannin "Like" ka nuna goyon baya ko kuma "Share" ka yaɗa shafin



Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub